Isaiah 22:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَمَرْ يَدَّ عَكَنْ رَاتَيَ تُݣُونٜىٰ دَ ݣُونُواْنِ دَ ݣُوڢْ دَ تُلُنَ عَڧُوسَرْ دَ عَكَ كَڢَ عَبَنْغُواْ، حَكَ ذَاعَ رَاتَيَ مَسَ دُكَنْ حَكِّنْ غِدَنْ كَكَنْسَ دَ دُكَنْ ذُرِيَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Amma dukan 'yan'uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya!