Isaiah 22:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar giggicewa da tattakewa da banrazana a cikin Kwarin Wahayi, ranar ragargazawar katanga da ta yin kuka ga duwatsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِ، رَانَ ثٜىٰ دَ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا يَكَٰوُاْ، رَانَرْ تَاشِنْ حَنْكَلِ دَ رُوطٜىٰوَ دَ ضِكِثِيوَ أَ ݣُورِنْ غَنِنْ رُعُيَ، رَانَرْ رُشٜىٰ كَتَنْغَرْ بِرْنِنْ عُرُوشَلِيمَ، رَانَرْ كُوكَنْ نٜىٰمَنْ تَيْمَكُواْ دَغَ تُدُنْ سِهِيُواْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.