Isaiah 23:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ «يَا كٜىٰ بُدُرْوَ، ذُوثِيَاتَ سِدُوانْ، أَيَّ، ڢَضٍ ثِكِنْكِ يَڧَارٜىٰ، مُتَنٜىٰنْكِ سُنَ ثِكِنْ دَنِّيَ؞ كِتَاشِ كِڧٜىٰتَرٜىٰ ذُوَا سَيِڢُرُسْ، عَمَّا كُواْ عَثَنْ مَا بَذَاكِ هُوتَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama'arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.