Isaiah 23:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُوبِے مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ بَابِيلَ، دَا أَنْسَنْ دَسُو عَمَّا يَنْذُ بَاسَ نَنْ؞ أَسُّرِيَاوَا سُكَ مَيْدَ عِتَ وُرِنْ ذَمَنْ نَمُواْمِنْ دَاجِ؞ سُكَ غِنَا أَبِنْ هَوَنْ كَتَنْغَ دُوانْ يَاڧِ، سُكَ رُرُّشٜىٰ غِدَاجٜىٰنْ سَرَاكُنَنْتَ، سُكَ مَيْدَ بِرْنِنْ كُڢَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
(Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)