Isaiah 24:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haka zai zama a duniya da kuma a cikin al’ummai, kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun, ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا يَدَّ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ عَدُونِيَا، كُمَ عَثِكِنْ أَلْعُمَّنْ دُونِيَا؞ أَيْ، یَنْ كَطَنْ نٜىٰ ذَاسُ ضَغٜىٰ، كَمَرْ ضَغُواْوَرْ یَیَنْ إِتَاثٜىٰنْ ظَيْتُنْ دَ عَكَ كَكَّٻٜىٰ، كَمَرْ غُواْنَرْ إِنَبِنْدَ عَكَيِ كَالَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan shi ne abin da zai sami kowace al'umma ko'ina a duniya. Zai zama kamar ƙarshen kaka sa'ad da aka karkaɗe zaitun daga kowane itace, aka kuma gama tsinke 'ya'yan inabi daga kurangar inabi.