Isaiah 24:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga ƙarar razana zai fāɗa cikin rami; wanda kuma ya tsere daga rami za a kama shi a tarko. An buɗe ƙofofin ambaliyar ruwan sama, harsashen ginin duniya suna rawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَغُدُ دَغَ أَبِنْ ڟُواْرُواْ، ذَيْ ڢَاطَ ثِكِنْ رَامِ؞ وَنْدَ كُمَ يَكُٻُتَ دَغَ ثِكِنْ رَامِ ذَيْ ڢَاطَ ثِكِنْ تَرْكُواْ؞ غَمَا تَغُواْغِنْ سَمَّيْ ذَاسُبُوطٜىٰ، تُوشٜىٰنْ دُونِيَا كُمَ ذَيْ غِرْغِظَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk wanda ya yi ƙoƙarin tserewa daga razana zai fāɗa cikin wushefe, wanda kuma ya tsere daga wushefe za a kama shi a tarko. Za a kwararo ruwa daga sama kamar da bakin ƙwarya, harsashin ginin duniya zai jijjigu.