Isaiah 25:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane, liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ذَيْ شِرْيَ بِكِ؞ عَكَنْ وَنَّنْ بَبَّنْ تُدُ ذَيْ شِرْيَ وَدُكَنْ ڧَبِيلُ بِكٍ عَبِنْثِ مَڢِے ݣَوْ، بِكٍ ضُوً إِنَبِے مَڢِے ݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.