Isaiah 28:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai zama ruhun adalci gare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a, wurin samun ƙarfi ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ ذَيْبَادَ رُوحٌ يِنْ أَدَلْثِے غَ مَيْ شَرِيعَ، ڧَرْڢِنْ حَلِ كُمَ غَ مَاسُ ڟَرٜىٰ ڧُواْڢَرْ بِرْنِ دَغَ أَبُواْكَنْ غَابَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.