Isaiah 3:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَيْمَكُوانْ ڧَنْشِ، ذَاعَ جِ وَرِ، مَيْمَكُوانْ أَبِنْ طَمَرَ، سَيْ إِغِيَرْ ثِيَوَ، مَيْمَكُوانْ أَدُوانْ كِڟُواْ، سَيْ كَنْ عُنْغُلُ، مَيْمَكُوانْ بَبَّرْ رِغَا، سَيْ ڟُمُّواْكِ، مَيْمَكُوانْ ݣَنْ غَنِ، سَيْ مُونِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Maimakon su riƙa ƙanshin turare, za su yi wari, a maimakon abin ɗamara, za su yi ɗamara da igiyoyi masu kaushi, a maimakon su kasance da kyakkyawan gashi, za su zama masu sanƙo, a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki, kyansu zai zama abin kunya!