Isaiah 30:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَمْسَرْ مَيْ ڟَرْكِنَّنْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، «سَبُواْدَ كُنْڧِ سَڧُواْنَّنْ نَوَ، كُكَ دُواْغَضَ غَ دَنِّيَ دَ رُوطُ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba.