Isaiah 30:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْدَ حَكَمَا وَتَ ذَيْ يِ حَصْكٜىٰ كَمَرْ رَانَ، رَانَ كُمَ ذَاتَ ڧَارَ حَصْكٜىٰنْتَ حَرْ سَوْ بَݣَويْ، كَمَرْ أَنْتَتَّارَ حَصْكٜىٰنْ رَانَ نَݣُونَ بَݣَويْ أَ رَانَ طَيَ؞ وَنَّنْ ذَيْ ڢَرُ نٜىٰ أَ رَانَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَارَ طَطَّوْرَ مِيكِنْ مُتَنٜىٰنْسَ يَكُمَ وَرْكَرْدَ رَوْنُكَنْ دَ يَيِ مُسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa'ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.