Isaiah 32:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُيِ ضَوَرْ جِكِے دُواْمِنْ ڟُواْرُواْ، كُو مَاتَا مَاسُ ذَمَنْ جِنْ دَاطِے، كُجِجِّغُ، كُو دَ كُكٜىٰيِنْ ذَمَنْكُ أَ سَكٜىٰ! كُتُوٻٜىٰ كَايَنْكُ، كُطَوْرَ رِيغُنَنْ نُونَ بَڧِ ثِكِ عَݣُونْݣُوسُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.