Isaiah 33:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shi da yake tafiya cikin adalci yana kuma magana abin da yake daidai, wanda yake ƙin riba daga cuta yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci, wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنْدَ ذَيْ عِيَ، شِينٜىٰ مَيْ تَڢِيَ ثِكِنْ أَدَلْثِے، مَيْ ڢَطِنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ دَيْدَيْ، مَيْ ڧِنْ ڧَظَامَرْ رِيبَ، مَيْ ڧِنْ كَرْٻَرْ ثِنْ حَنْثِ، مَيْ ڧِنْ جِنْ ڧُلّٜىٰ ڧُلّٜىٰنْ كِسَنْ كَيْ، مَيْ ڧِنْ تُنَانِنْ عَيْكَتَ مُغُنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.