Isaiah 34:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بِنْثِكَ ثِكِنْ لِتَّڢِنْ يَهْوٜىٰهْ كَكَرَنْتَ، «بَابُ طَيَ وَدَّ ذَاتَ ٻَثٜىٰ، بَابُ طَيَ وَدَّ ذَاتَ رَسَ أَبُواْكِنْ ذَمَ؞ غَمَا دَ بَاكِنْسَ يَهْوٜىٰهْ يَبَادَ عُمَرْنِ رُوحُنْسَ نٜىٰ كُمَ يَتَتَّرَاسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bincika cikin Littafin Ubangiji ka karanta abin da yake faɗa. Ba ko ɗaya cikin halittattun nan da zai ɓata ba, ba kuwa wanda zai rasa ɗan'uwansa. Ubangiji ne ya umarta ya zama haka, shi kansa zai kawo su tare.