Isaiah 36:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَعَيْكَ دَ وَكِيلِنْسَ دَغَ بِرْنِنْ لَكِشْ ذُوَا وُرِنْ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ أَ عُرُوشَلِيمَ، تَرٜىٰدَ بَبَّرْ ڧُنْ‌غِيَرْ سُواْجُواْجِ؞ سَيْ وَكِيلِنْ يَڟَيَ أَ لَمْبَتُنْ دَيَكٜىٰ كَٰوُاْ ضُوَ دَغَ تَڢْكِ نَتُدُ، كُسَدَ حَنْيَرْ ڢِيلِنْ مَاسُ وَنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya umarci babban shugaban yaƙinsa ya tashi daga Lakish ya tafi Urushalima tare da babbar rundunar mayaƙa don su sa sarki Hezekiya ya ba da kai. Sai shugaban ya mamaye hanya inda masu wankin tufafi suke aiki, a daidai magudanar da yake kawo ruwa daga kududdufin da yake daga can bisa.