Isaiah 36:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka ce kana da dabara da kuma ƙarfin mayaƙa, amma kana magana banza ce kawai. Ga wa ka dogara, da kake tayar mini?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَنَ ڟَمَّنِ مَغَنَ دَ بَاكِ كَوَيْ عِتَثٜىٰ دَبَرَرْ يَاڧِ دَ ڧَرْڢِنْ يَاڧِ؟ عَكَنْ وَ كَكٜىٰ دُواْغَضَ يَنْذُ دَ حَرْ ذَاكَيِ مِنِ تَاوَيٜىٰ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce, “Kana tsammani magana da baki kawai ta isa ta yi aiki da gwanayen sojoji, da kuma masu ƙarfi? Wa kake tsammani zai taimake ka, har da za ka yi mini tawaye?