Isaiah 36:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yaya za ka ƙi hafsan mafi ƙanƙanci na hafsoshin maigidana, ko da yake kana dogara ga Masar don kekunan yaƙi da mahayan dawakai?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاكُ عِيَ ثِنْ نَصَرَا عَكَنْ سُواْجَ مَڢِے ڧَنْڧَنْتَ نَشُوغَبَانَ بَ، كُواْدَيَكٜىٰ كَنَ دُواْغَضَ عَكَنْ مَصَرْ سُبَاكَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِنْ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba ka yi daidai da ka ƙi ko wani marar maƙami a shugabannin Assuriya ba, duk da haka kana sa rai ga Masarawa su aiko maka da karusai, da mahayan dawakai!