Isaiah 37:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَكَسَكُنّٜىٰ كَجِ، كَبُوطٜىٰ عِدَنُونْكَ كَغَنِ، كَسَوْرَرِ مَغَنْغَنُنْ غُواْرِنْ دَ سَرْكِے سٜىٰنَّكٜىٰرِبْ يَكٜىٰيِ مَكَ، كَيْ اللَّهْ مَيْ رَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Senakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai.