Isaiah 37:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعَيْكَ عٜىٰلِيَكِمْ شُوغَبَنْ غِدَنْ سَرْكِے دَ شٜىٰبْنَ مَرُبُوثِ، تَرٜىٰدَ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے، دُكَنْسُ سَنْيٜىٰ دَ رِيغُنَنْ نُونَ بَڧِنْ ثِكِ، ذُوَا وُرِنْ أَنَّبِے عِشَايَ طَنْ أَمُواظْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya aiki Eliyakim mai kula da fāda, da Shebna marubucin ɗakin shari'a, da manyan firistoci zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Su kuma suna saye da tsummoki.