Isaiah 37:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta wurin jakadunka ka jibge zage-zage a kan Ubangiji. Ka kuma ce, ‘Da kekunan yaƙina masu yawa na hau ƙwanƙolin duwatsu, ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon. Na sassare al’ul mafi tsayi fir mafi kyau. Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَیَنْ عَيْكَنْكَ كَيِ وَ عُبَنْغِجِ غُواْرِ؞ كَثٜىٰ تَيَوَنْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِنْكَ كَهَوْ كَنْ تُدَّيْ مَڢِے ڟَيِ، حَرْ إِيَاكَرْ ڟَوُانْ تُدَّنْ لٜىٰبَنُوانْ؞ كَݣُونْتَرْ دَ عِتَتُوَنْ سٜىٰدَ مَڢِے ڟَيِ، دَ عِتَتُوَنْ ڢِرْ مَڢِے ݣَوْ؞ كَثٜىٰ كَكَيْ إِيَاكَرْ تُدَّنْ لٜىٰبَنُوانْ، كَشِغَ ثِكِ ثِكِنْ كُرْمِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.