Isaiah 37:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ba ka ji ba cewa tun dā can na shirya ya zama haka? A kwanakin dā na kafa shi; yanzu na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu mafaka zuwa tsibin ɓuraguzai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹بَكَجِبَ؟ تُنْ تُنِ نَشِرْيَ حَكَ ذَيْ ڢَرُ؞ تُنْ ݣُونَكِنْ دَا نَشِرْيَ أَبِنْدَ نَكٜىٰ ثِكَاوَا يَنْذُ، وَتُواْ يَدَّ ذَاكَ مَيْدَ بِرَنٜىٰ مَاسُ كَتَنْ‌غَ كُڢَيْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.