Isaiah 37:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَسَامِ لَابَرِ ثٜىٰوَ سُواْجُواْجِنْ مَصَرْ عَڧَرْڧَشِنْ شُوغَبَنْثِنْ سَرْكِے تِرْهَكَ نَ إِتِيُواْڢِيَ سُنْ ڢِتُواْ دُواْمِنْ سُيَاڧٜىٰشِ؞ سَيْ سَرْكِے يَعَيْكَ دَ یَنْ عَيْكَ ذُوَا وُرِنْ هٜىٰزٜىٰكِيَ ثٜىٰوَ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Assuriyawa suka ji, cewa mayaƙan Masarawa, waɗanda sarki Tirhaka na Habasha take yi wa jagora, suna zuwa su far musu da yaƙi. Sa'ad da sarkin ya ji haka sai ya aika wa sarki Hezekiya da wasiƙa,