Isaiah 39:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ishaya annabi ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya kuma tambaye shi ya ce, “Mene ne waɗannan mutane suka faɗa, kuma daga ina suka fito?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Sun zo ne daga Babilon.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَنَّبِے عِشَايَ يَذُواْ وُرِنْ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَثٜىٰ مَسَ «دَغَ إِنَا نٜىٰ مُتَنٜىٰنَّنْ سُكَ ڢِتُواْ؟ مٜىٰنٜىٰنٜىٰ كُمَ سُكَثٜىٰ مَكَ؟» هٜىٰزٜىٰكِيَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «سُنْ ذُواْ وُرِينَ نٜىٰ دَغَ وَتَ ڧَسَا مَيْ نِيسَ، وَتُواْ دَغَ ڧَسَرْ بَابِيلَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”