Isaiah 4:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَهْوٜىٰهْ ذَيْسَا ڧُنْشِنْ غِرْغِجٜىٰ يَرُڢٜىٰ دُكَنْ بَبَّنْ تُدُنْ سِهِيُواْنَ دَ وُرِنْ تَارُوانْ جَمَعَرْسَ دَ رَانَ؞ دَ دَرٜىٰ كُمَ ذَيْ كَٰوُاْ هَيَاڧِے دَ ڧُنْشِنْ وُتَا مَيْ حَصْكَكَاوَا؞ حَڧِيڧَ، طَوْكَكَرْسَ ذَاتَ رُڢٜىٰ بِرْنِنْ دُكَ كَمَرْ تٜىٰنْتِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan a kan Dutsen Sihiyona, da a kan dukan waɗanda suka tattaru a can, Ubangiji zai aika da girgije da rana, hayaƙi da hasken harshen wuta kuma da dare. Darajar Ubangiji za ta rufe, ta kuma kiyaye birnin duka.