Isaiah 40:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمْ مَيْ تَلَوْثِ يَكَنْ ذَاٻِ إِتَاثٜىٰنْ دَ بَذَيْ ضُٻَبَ؞ يَكَنْ نٜىٰمِ ڠُونِنْ عَيْكِنْ حَنُّ يَكَڢَ مَسَ غُنْكِنْ دَ بَذَيْ ڢَاطِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutum wanda bai isa samun azurfa ko zinariya ba, Yakan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yana neman gwanin sassaƙa Domin ya yi masa siffa wadda ba za ta fāɗi ba.