Isaiah 40:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيْ مَيْ كَٰوُاْ لَابَرِ مَيْ دَاطِے غَ سِهِيُواْنَ، سَيْ كَهَوْرَ بَبَّنْ تُدُ مَيْ ڟَيِ، كَتَادَ مُرْيَرْكَ دَ ڧَرْڢِے؞ كَيْ مَيْ كَٰوُاْ لَابَرِ مَيْ دَاطِے غَ عُرُوشَلِيمَ، كَطَغَ مُرْيَرْكَ، كَدَ كَجِڟُواْرُواْ؞ كَسَنَرْوَ غَرُضُوً يَهُودَ ثٜىٰوَ «دُوبَ! غَا اللَّهْ نْكُ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ki haura a kan dutse mai tsayi, ke Urushalima, Ki faɗi albishir! Ki yi kira da babbar murya, ya Sihiyona, Ki faɗi albishir! Yi magana da ƙarfi, kada kuwa ki ji tsoro. Ki faɗa wa garuruwan Yahuza, Cewa Allahnsu yana zuwa!