Isaiah 41:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْسَا عِتَتُوَنْ سٜىٰدَ دَ نَأَكَشِيَ، دَ نَمُرْتِلْ دَ نَظَيْتُنْ، سُيِ غِرْمَ أَدَاجِ مَرَرْ كُواْمٜىٰ؞ ذَنْ كُمَسَا إِتَاثٜىٰنْ سَيِڢِرِسْ دَ نَڢِرْ، دَ نَدَبِينُواْ سُذَمَ كُرْمِ أَ هَمَادَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan sa itatuwan al'ul su tsiro a hamada, Da itacen ƙirya, da itacen ci-zaki, da zaitun. Ƙeƙasasshiyar ƙasa za ta zama kurmi, Jejin itatuwan fir.