Isaiah 41:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Na zuga wani daga arewa, ya kuwa zo, wani daga inda rana ke fitowa wanda yake kira bisa sunana. Yana takawa a kan masu mulki kamar da taɓarya, sai ka ce maginin tukwane yana taka laka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«نَذَاٻِ وَنِ مَيْ ذَمَ أَغَبَسْ، يَنَ كُوَ ذُوَا، نَتَادَ وَنِ مَيْ كِرَا غَ سُونَنَ، يَنَ كَٰوُاْ يَاڧِ دَغَ أَرٜىٰوَ؞ يَنَ تَتَّاكٜىٰ سَرَاكُنَ كَمَرْ لَاكَ، كَمَرْ يَدَّ مَيْ غِنِنْ تُݣُونٜىٰ يَكٜىٰ تَتَّاكٜىٰ لَكَرْ غِنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Na zaɓi mutum wanda yake zaune a gabas, Zan kawo shi don ya kawo hari daga arewa. Zai tattake masu mulki su zama kamar lāka, Kamar yadda magini yake tattake yumɓu.