Isaiah 43:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Namun jeji suna girmama ni, diloli da mujiyoyi ma haka, domin na tanada musu ruwa a hamada da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa, don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَمُواْمِنْ دَاجِ ذَاسُ غِرْمَمَنِ، دُكْ دَ كَرْنُكَنْ دَاجِ دَ جِمِنُ، غَمَا نَا بَادَ ضُوَ أَدَاجِ عِنْدَ بَابُ كُواْوَ، رَاڢُڢُّكَ كُمَ عَثِكِنْ هَمَادَ، دُواْمِنْ إِنْبَادَ ضُوَنْشَا غَ مُتَنٜىٰنَ دَ نَذَاٻَا،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har da namomin jeji za su girmama ni, Diloli da jiminai za su yi yabona Sa'ad da na sa kogunan ruwa su yi gudu a hamada, Domin su ba da ruwa ga zaɓaɓɓun mutanena.