Isaiah 43:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ دُكَنْ أَلْعُمَّيْ سُتَتَّارُ وُرِے طَيَ، بَرِ ڧَبِيلُ سُتَارُ؞ وَنٜىٰنٜىٰ عَثِكِنْسُ يَڢَطِ أَبُبُوَنَّنْ؟ وَنٜىٰنٜىٰ يَيِ أَنَّبْثِنْ أَبُبُوَنْدَ سُكَ وُثٜىٰ؟ بَرِ سُكَٰوُاْ شَيْدُنْسُ سُتَبَّتَرْ مَنَ غَسْكِيَرْسُ، بَرِ شَيْدُنْ سُسَوْرَرَ، سُيِ شَيْدَ ثٜىٰوَ «عِ، حَكَ يَكٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kirawo sauran al'umma, su zo ga shari'a. A cikin allolinsu wane zai iya faɗar abin da yake a gaba? A cikinsu wa ya yi hurci a kan abin da yake faruwa yanzu? Bari waɗannan alloli su kawo shaidunsu Don su tabbatar daidai suke, Su shaida gaskiyar maganganunsu.