Isaiah 44:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ، إِرِنْ مُتُمِنَّنْ دَ مُتَنٜىٰنْسَ ذَاسُشَا كُنْيَا؞ مَاسُ ڧٜىٰرَ غُمَكَ، یَنْ أَدَمْ نٜىٰ كَوَيْ؞ بَرِ دُكَنْسُ سُتَارُ سُڟَيَ أَغَبَنْ كُواْتُ؞ أَيْ، ذَاعَ ڟُواْرَتَرْ دَسُو، ذَاسُ كُوَ شَا كُنْيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan wanda ya yi mata sujada za a ƙasƙantar da shi. Mutanen da suka ƙera gumakan, 'yan adam ne, ba wani abu ba. Bari su zo su tsaya gaban shari'a, za su razana, su kuma sha kunya.