Isaiah 44:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kafinta yakan gwada katako yă kuma zāna siffar da alli; yă goge shi da kayan aiki yă kuma zāna shi da alƙalami. Yă siffanta shi a kamannin mutum, mutum cikin dukan darajarsa, don yă ajiye shi a cikin masujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْتَ يَكَنْ عَوْنَ إِتَاثٜىٰ، يَظَانَ صِڢَّ دَ أَبِنْ ذَانِ، سَعَنً يَسَسَّڧَ شِ دَ كَايَنْ عَيْكِنْسَ، يَيِ شِ دَ صِڢَّرْ مُتُمْ ݣَكْݣَاوَا، دُواْمِنْ عَكَڢَ شِ أَوُرِنْ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Masassaƙi yakan auna itace. Ya zana siffa da alli, sa'an nan ya sassaƙe shi da kayan aikinsa. Ya yi shi da siffar mutum kyakkyawa, domin a ajiye shi a masujadarsu.