Isaiah 44:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَكَنْ سَارٜىٰ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ، كُواْ يَذَاٻِ إِتَاثٜىٰنْ ڢِرْ كُواْ إِتَاثٜىٰ مَيْ ڧَرْڢِے؞ يَكَنْ بَرْ إِتَاثٜىٰنْ يَيِ غِرْمَ دَ ڧَرْڢِے عَثِكِنْ عِتَتُوَنْ كُرْمِ، كُواْ كُوَ يَشُوكَ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ يَبَرْ ضُوً سَمَ يَسَا إِتَاثٜىٰنْ يَيِ غِرْمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai yiwu ya sare itacen al'ul ya yi da shi, ko kuwa ya zaɓi itacen oak, ko na kasharina daga jeji. Ko kuwa ya dasa wani itace, ya jira ruwan sama don ya sa itacen ya yi girma.