Isaiah 44:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ وَنِ سَاشٜىٰ كُمَ يَكَنْ هُورَ وُتَا دُواْمِنْ يَغَسَ نَامَ، يَثِ، يَڧُواْشِ؞ يَكَنْجِ طُمِ حَرْ يَثٜىٰ، «كَيْ، طُمِنَّنْ يَنَدَ دَاطِے، وُتَرْ نَنْ تَنَدَ ݣَوْ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yakan hura wuta da wani sashi domin ya gasa nama, ya ci, ya ƙoshi. Ya ji ɗumi ya ce, “Kai, ɗumi da daɗi, wutar tana da kyau!”