Isaiah 44:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِنٜىٰ نَاثٜىٰ وَ سَرْكِے سَيِرُسْ، ‹غَاشِ، نَامَيْدَكَيْ مَكِيَايِ، كَيْنٜىٰ ذَاكَ ثِكَ دُكَنْ مَنُڢَاتَ؞› نِنٜىٰ نَابَادَ عُمَرْنِ ثٜىٰوَ ‹أَ سَاكٜىٰغِنَ عُرُوشَلِيمَ، عَكُمَ كَڢَ تُوشٜىٰنْ غِنِنْ هَيْكَلِنْ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina, Za ka yi abin da nake so ka yi, Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima, A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”