Isaiah 44:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ مَاسُ يِنْ غُمَكَ بَنْظَنٜىٰ، غُمَكَنْسُ دَسُكٜىٰيِنْ ڢَضٍ ثِكِ عَكَنْسُ، بَاسُ دَ أَمْڢَانِ؞ سُو دَسُكٜىٰ بَوْتَرْ غُمَكَ، مَكَڢِ نٜىٰ سُو، جَهِلَيْ كُمَ، ذَاسُشَا كُنْيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.