Isaiah 45:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِنٜىٰ نَا يِدُونِيَا، نَكُمَ حَلِثِّ یَنْ أَدَمْ عَثِكِنْتَ؞ دَ إِيكُوانْ هَنُّونَ نَا شِمْڢِطَا سَمَّيْ، إِنَ كُوَ يِنْ مُلْكِ عَكَنْ رَانَ دَ وَتَ دَ تَوْرَرِ دُكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni ne wanda ya halicci duniya, Na kuma halicci mutum don ya zauna cikinta. Da ikona na shimfiɗa sammai, Ina kuwa mallakar rana, da wata, da taurari.