Isaiah 45:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku tattaru ku zo; ku taru, ku masu gudun hijira daga al’ummai. Masu jahilci ne waɗanda suke ɗaukan gumakan katakai suna yawo, waɗanda suke addu’a ga allolin da ba za su cece su ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ، «كُتَتَّارُ وُرِے طَيَ دُواْمِنْ شَرِيعَ، كُتَارُ، كُو ضَغُواْوَرْ أَلْعُمَّنْ دَ كُكَ ڟِيرَا! مَرَسَ سَنِ نٜىٰ وَطَنْدَ سُكٜىٰطَوْكٜىٰ دَ غُمَكَنْسُ نَ إِتَاثٜىٰ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ أَدُّعَ غَ أَلُّواْلِنْ دَ بَذَاسُ عِيَ ثٜىٰتُوانْسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Ku taru wuri ɗaya ku jama'ar al'ummai, Dukanku da kuka tsira daga faɗuwar mulki, Ku gabatar da kanku domin shari'a! Waɗancan da suka ɗauka gumakansu na itace, Suna kuma addu'a ga allolin da ba su iya cetonsu, Waɗannan mutane ba su san kome ba ko kaɗan!