Isaiah 46:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bel ya rusuna, Nebo ya durƙusa ƙasa; ana ɗaukan gumakansu a kan dabbobi ne. Siffofin da ake yawo da su nawaya ne, kayan nauyi masu gajiyarwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غُنْكِنَّنْ بٜىٰلْ يَدُرْڧُسَ، غُنْكِنَّنْ نٜىٰبُواْ، شِے مَا يَسُنْكُيَ؞ غَاشِ، أَنَ طَوْكَرْسُ عَكَنْ جَاكُنَ، أَنَ لُواْدِنْسُ عَكَنْ دَبُّواْبِے؞ سُنْ ذَمَ كَايَ مَيْ نَوْيِ عَكَنْ دَبُّواْبِنْ دَ سُكَ غَجِ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Wannan ne ƙarshen allolin Babila! Dā ana yi wa Bel da Nebo sujada, Amma yanzu ana labtunsu a kan jakuna, Sun zama nawaya a kan dabbobin da suka gaji!