Isaiah 46:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sukan daga shi a kafaɗunsu su kuma ɗauke shi; sukan kafa shi a tsaye a wurinsa, a can kuwa zai tsaya. Daga wannan wuri ba zai iya gusawa ba. Ko da wani ya nemi taimakonsa, ba ya amsawa; ba zai iya cetonsa daga wahala ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَنْ طَغَ غُنْكِنْ عَكَڢَطَرْسُ سُطَوْكِ نَوْيِنْسَ، سُكَنْ سَامِ وُرِے سُسَاشِ، يَڟَيَ، دَغَ وُرِنْ دَ عَكَسَا شِ، بَايَ عِيَ مُواْڟِ؞ كُواْ دَ وَنِ يَيِ مَسَ كُوكَنْ نٜىٰمَنْ تَيْمَكُواْ، بَايَ عِيَ أَمْسَاوَا، بَايَ عِيَ ثٜىٰتُوانْ مُتُمْ دَغَ وَهَلَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka ɗauke shi a kafaɗunsu su tafi da shi, Suna ajiyewa a wani wuri, ya yi ta tsayawa a can, Ba ya iya motsawa daga inda yake. Idan wani ya yi addu'a gare shi, ba zai iya amsawa ba, Ko ya cece shi daga bala'i.