Isaiah 47:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai! Bari masananki na taurari su zo gaba, waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata, bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كِنْ رِغَا كِنْ غَجِ دَ يَوَنْ شَوَرَرْ دَ عَكٜىٰ بَاكِ! بَرِ مَاسُ بِنْثِكٜىٰنْ تَوْرَرِ دَ مَاسُ بِنْثِكٜىٰنْ سَرَرِنْ سَمَ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ مِكِ شٜىٰلَرْ أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ، سُتَاشِ سُثٜىٰثٜىٰكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi. Bari mashawartanki su fito su cece ki, Waɗancan mutane masu binciken taurari Waɗanda suka zana taswirar sammai, Su kuma faɗa miki Dukan abin da zai faru da yake wata wata.