Isaiah 47:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دُكَنْ أَبُبُوَنَّنْ بِيُ ذَاسُ ڢَرُ دَكٜىٰ بَا لَابَرِ أَ رَانَ طَيَ، ذَاكِ رَسَ یَیَنْكِ، كِذَمَ كَمَرْ مَثٜىٰنْ دَ مِجِنْتَ يَمُتُ؞ وَنَّنْ ذَيْ ڢَرُ دُكْ دَ يَوَنْ سِحِرِنْكِ، دُكْ دَ إِيكُوانْ بُواْكَنْثِنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya Dukan waɗannan al'amura za su faru. Kome sihirin da za ki yi, Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.