Isaiah 48:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُنْجِ غَمٜىٰدَ أَبُبُوَنَّنْ، كُكَ كُمَ غَ ثِكَاوَرْسُ، تُواْ، بَذَاكُ أَمِنْثٜىٰ نَڢَطِ غَسْكِيَ عَكَنْسُبَ؟ يَنْذُ ذَنْسَا كُجِ سَابَبِّنْ أَبُبُوَ، أَبُبُوَ نَأَسِيرِ وَطَنْدَ بَكُ تَٻَ سَنِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Dukan abin da na faɗa yana cika yanzu, Sai ku yarda, faɗata gaskiya ce. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwan da za su zo, Abubuwan da ban bayyana su a dā ba.