Isaiah 49:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاسُ تَٻَ جِنْ يُنْوَ كُواْ ڧِشِبَ، بَذَاسُ شَا ذَاڢِنْ رَانَ كُواْ نَدَاجِنْ يَشِبَ، غَمَا شِے مَيْ تَوْسَيِنْسُ نٜىٰ ذَيْبِيدَسُو، ذَيْبِيدَسُو ذُوَا مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba. Ba za su sha zafin rana da na hamada ba, Gama wanda yake ƙaunarsu ne zai bi da su. Zai bi da su zuwa maɓuɓɓugan ruwa.