Isaiah 49:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan ’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كِطَغَ عِدَنُونْكِ سَمَ، كِدُوبَ كٜىٰوَيٜىٰ كِغَنِ، یَیَنْكِ سُنَ تَتَّارُوَ سُنَ دَاوُاْوَ غِدَا؞ حَڧِيڧَ، نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ضَنْڟٜىٰ دَ رَيْنَ ثٜىٰوَ یَیَنْكِ ذَاسُ ذَمَ مِكِ كَمَرْ كَايَنْ أَدُواْ، ذَاكِيِ تَاڧَمَ دَسُو كَمَرْ يَدَّ أَمَرْيَ تَكَنْيِ دَ أَدُوانْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ki dudduba, ki ɗaga idonki, ki ga abin da yake faruwa! Mutanenki suna tattaruwa suna komowa gida! Hakika, da yake ni ne Allah Mai Rai, Za ki yi fāriya da mutanenki, Kamar yadda amarya take fāriya da kayan adonta!