Isaiah 49:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa, “I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa, a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro; zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke, zan kuwa ceci ’ya’yanki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاشَكَّ، إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، «ذَاعَ كُٻُتَرْدَ وَطَنْدَ عَكَ كَامَ عَيَاڧِ، ذَاعَ ڨُوثٜىٰ كَايَنْ دَ مَرَرْ تَوْسَيِ يَݣُوشٜىٰ؞ غَمَا نِے ذَنْيِ غَابَادَ دُكْ مَيْ غَابَادَكٜىٰ، ذَنْكُوَ كُٻُتَرْدَ یَیَنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya amsa ya ce, “Wannan shi ne ainihin abin da zai faru. Za a ƙwace kamammun yaƙi, Za a kuma ƙwace wason da masu baƙin mulki ya yi. Zan yi yaƙi da dukan wanda yake yaƙi da ku, Zan kuwa kuɓutar da 'ya'yanku.