Isaiah 5:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta domin rashin fahimi; manyan mutanensu za su mutu da yunwa talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ وَنَّنْ رَشِنْ سَنِ مُتَنٜىٰنَ ذَاسُ تَڢِے بَوْتَا، مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْسُ ذَاسُ مُتُ دَ يُنْوَ، تَلَكَاوَنْسُ كُمَ ذَاسُ بُوشٜىٰ دَ ڧِشِنْ ضُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.