Isaiah 50:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma yanzu fa, dukanku waɗanda kuke ƙuna wuta kuna kuma tanada wa kanku fitilu masu ci, ku je ku yi tafiya a cikin hasken wutarku da na fitilun da kuka ƙuna. Abin da za ku karɓa ke nan daga hannuna. Za ku kwanta a cikin azaba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ، كُو دَ كُكٜىٰ هُورَ وُتَا، كُنَ تَنَدَ وَكَنْكُ حَصْكٜىٰنْ ڢِتِلُ، سَيْ كُيِ تَڢِيَ ثِكِنْ حَصْكٜىٰنْ وُتَرْكُ، دَ نَڢِتِلُنْ دَ كُكَ كُنَّ؞ غَا أَبِنْدَ ذَنْيِ مُكُ دَ هَنُّونَ، ذَاكُ ݣُونْتَ ثِكِنْ عَذَابَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukanku da kuke ƙulle-ƙullen hallaka juna Ƙulle-ƙullenku za su hallaka ku! Ubangiji kansa zai sa wannan ya faru, Za ku gamu da mummunar ƙaddara.