Isaiah 52:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كِتَاشِ، كِتَاشِ! يَا سِهِيُواْنَ، كِڧَرْڢَڢَ كَنْكِ! كِسَنْيَ رِيغُنَنْكِ مَاسُ ݣَوْ، يَا عُرُوشَلِيمَ بِرْنِ مَيْ ڟَرْكِے؞ غَمَا أَرْنَ مَرَسَ كَاثِيَ دَ مَاسُ ڧَظَنْتَا بَذَاسُ سَاكٜىٰ شِغَ تَڧُواْڢُواْڢِنْكِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Urushalima, ki ƙarfafa, ki yi girma kuma! Birni mai tsarki na Allah, Ki yafa wa kanki jamali! Arna ba za su ƙara shiga ta ƙofofinki ba.