Isaiah 53:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاوَنْ يَيِ غِرْمَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ كَمَرْ طَنْ ڟِرُواْ، كَمَرْ تُوشٜىٰنْدَ يَڟِيرَا عَبُوسَشِّيَرْ ڧَسَا؞ بَ شِ دَ صِڢَّ مَيْݣَوْ كُواْ دَرَجَرْ دَ ذَاتَ جَا حَنْكَلِنْمُ وُرِنْسَ، بَ شِ دَ كَمَنِّ مَيْ شَعَوَرْ غَنِنْ دَ ذَيْسَا مُسُواْ شِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin Da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.